Nijar; ''Za mu hana Boko Haram sakewa''

Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jamhuriyar Nijar ta sha fama da hare-haren 'yan Boko Haram musamman a garin Diffa.

Yayin da kasashen yankin tafkin Chadi ke ci gaba da daukar matakai domin dakile Boko Haram a yankin, hukumomi a jamhuriyar Nijar sun nanata cewa duk da cewa an karya lagon kungiyar ta Boko Haram, ba za su sake ba.

Yankin Diffa dai na shi ne ya yi fama da hare-haren kungiyar, kuma a halin da ake ciki jihar na karkashin dokar-ta-baci sanadiyar tarzomar Boko Haram.

Gwamnan jihar ta Diffa, Janar Abdu Kaza, ya yi wa wakilinmu, Ishaq Khalid, karin bayani a garin Diffa, kan irin matakan da jamhuriyar Nijar ta dauka da suka hana Boko Haram kama garuruwa a cikin kasar.

Janar Kaza ya shaidawa BBC cewa gwamnatin Nijar ta dauki matakan da suka hada da tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen kasar, da hadin kan da aka samu tsakanin gwamnatin Nigeria da Jamhuriyar Nijar ta yadda aka hada karfi da karfe a yakin da ake yi da kungiyar ta Boko Haram.