Shugabannin Cocin Katolika da na Orthodox sun gana

Image caption Fafaroma Francis da Patriach Kirill

Shugaban Cocin Katolika, Fafaroma Francis da takwaransa na Cocin Orthodox ta Rasha, Kiriil sun yi wata ganawarsu ta farko a tarihin Majami'un a cikin kusan shekara dubu da suka shude, bayan wani bambancin akidar da suka samu da ya yi sanadin darewarsu gida biyu.

Sun dai yi ganawar ne a Cuba, inda suka bukaci a kare mabiya addinin Kirista da ke Syria da sauran sassan da ke yankin gabas ta Tsakiya, wadanda suka ce ana kokarin shafe su a doron kasa.

Haka kuma sun ce akwai bukatar a taimaka da kayan agaji sosai don tallafa wa masu gudun-hijira daga Syria da Iraki.

Fafaroma Francis ya ce sun yi tattaunawar keke-da-keke, kuma watakila za su samu hanyar yin aiki tare, yayin da shi kuma shugaban Cocin Orthodox, Kiriil ke cewa duka sun dukufa ne wajen ba da gudummuwarsu wajen kare addinin Kirista.

ganawar da Kiriil ya yi da Fafaroma Francis babban ci gaba ne a yunkurin da ake yi na kawar da rashin jituwar da kuma zaman zargin da bangarori biyun suka shafe shekaru aru-aru suna yi da juna.