Saudiyya ta kai jiragen yaki Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saudiyya ta matso da jiragen saman yakin zuwa Turkiyya ne, domin ta matsa kaimi wajen kai hare-hare kan kungiyar IS, a cewar wani babban jami'in sojin kasar.

Saudiyya ta amsa cewa ta aika da jiragen saman yakinta zuwa wani sansanin soji a Turkiyya domin matsa kaimi a yakin da ta ke yi da IS a Syria.

Kafin yanzu, duk hare-haren da kasar ta ke kai wa, jiragen yakin daga filayen cikin kasarta ke tashi.

Kai jiragen da Saudia ta yi Turkiyya, ya sa sun matso kusa da inda suke kai hari a arewacin Syria.

Wani babban jami'in sojojin Saudiyyan ya ce, kasar ba ta tura wasu sojoji tare da jiragen yakin ba.

Sai dai ya kara da cewa rundunar sojojin kawance da ke karkashin Amurka ta yi amanna da cewa za a yi yakin kasa, kuma Saudiyya a shirye ta ke da a yi da ita.