Wajibi Rasha ta dakatar da hari a Syria

Hakkin mallakar hoto Getty

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace akwai bukatar Rasha ta sauya manufarta ta yin luguden wuta a Syria domin martaba yarjejeniya ta kawo karshen yakin.

Ya shaidawa shugabannin duniya a babban taron koli kan tsaro a Munich cewa sojojin Rasha suna kai hari kan kungiyoyin adawa da kuma fararen hula.

Yan adawar Syria sun ce ba za su bada kai bori ya hau ba.

Tun da farko Firaministan Faransa Manuel Valls ya bukaci Rasha ta daina yin ruwan bama bamai a kan fararen hula.

Sai dai Rasha ta ce babu wata shaidar da ta nuna cewa ta kai hari a kan fararen hula.

Firaministan Rasha Dmitri Medvedev yace tabarbarewar dangantaka tsakanin Rasha da kasashen yamma ta jefa duniya cikin wani yakin cacar baka.

Yace a kullum ana zargin Rasha da yin barazana ga NATO ko tarayyar turai ko Amurka ko kuma wasu kasashe.

Yace hadin kai ne kawai tsakanin Rasha da Amurka zai kai ga daidaituwar al'amura a Syria.