Dadadden mai shari'a a Amurka ya rasu

Mai sharia Antonin Scalia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mai shari'a Scalia ya dade a kotun kolin Amurka.

Dadden mai shari'a a kotun kolin Amurka mai shari'a Antonin Scalia ya rasu ya na da shekaru 79 a birnin Texas na kasar.

A shekarar 1986 ne shugaban Amurka na wancan lokacin Ronald Reagen ya nada Mai sharia Antonin Scalia a mukamin na sa, ya dai rasu ne ya na cikin bacci a jiya asabar a birnin Texas inda ya kai ziyarar Farauta kamar yadda ma'aikatar shari'ar Amurka ta sanar.

Shi ma shugaba Obama ya bayyana Mr Scalia da wani mutum ne da samun irin shi zai yi wuya saboda nagarta da karfin zuciya da ya ke da ita, da tsayawa kan gaskiya da kwarewa a aikinsa.

Shugaba Obama yace kara da cewa nan ba da jimawa ba zai maye gurbinsa da wanda ya dace, duk kuwa da kiraye-kirayen da 'yan jam'iyyar Republican ke yi na a dakatar da hakan har sai bayan an zabi sabon shugaban kasar Amurka.

Shugaba Obama ya ce yana da isasshen lokacin da zai yi hakan, kana kuma su ma 'yan majalisa su na da lokacin da za gudanar da aikinsu na bincike da amincewe da wanda za a nada kafin a kada kuri'a kan hakan.

Batun shugaban kasa ne ka dai ya ke da ikon nada Al-kalan kotun Koli ya dade ya na ci wa masu kada kuri'a a Amurkawa tuwo a kwarya Shekaru da dama inda suke ganin ya kamata su ma a ba su dama dan jin ra'ayin su.

Mutuwar mai shari'a Scadia wanda ya kasance dan jam'iyyar Republican mai ra'ayin mazan jiya kuma da ya fi dadewa a Kotun Kolin Amurka ta janyo cece kuce a kasar.

Inda 'yan jam'iyyar Republican a majalisar dokokin Amurka za su yi kokarin ko ta wanne hali shugaba Obama da suke ganin bai sauran watanni 11 ba wa'adin mulkinsa ya kare ya nada wanda zai maye gurbin Mi sharia Scadia ba.