'Yan tawayen Libya za su kafa gwamnati

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A halin da ake ciki dai gwamnatoci biyu ne ke ikirarin mulkin Libya.

Wakilan kungiyoyin 'yan tawayen Libya da ke taro a Morocco sun amince da wani kudurin kafa sabuwar gwamnati a karkashin wani shirin Majalisar dinkin duniya na kawo karshen rikicin da kasar ke fama da shi nan da shekara biyar masu zuwa.

An tura sunayen mutum 13, wadanda ake son nada musu mukamin minista zuwa majalisar dokokin kasar da ke Tobruk, wadda kasashen duniya suka amince da ita.

A baya dai majalisar ta ki amincewa da wani jerin sunayen mutum 32 da aka tura mata domin nada musu mukamin minista, tana cewa sun yi yawa.

A halin da ake ciki dai gwamnatoci biyu ne ke ikirarin mulkin Libya bayan rusa gwamnatin marigayi Kanar Gaddafi, yayin da kungiyar IS a bangare guda ke iko da wasu sassan kasar.