Fafaroma ya jagoranci addu'o'i a Mexico

Fafaroma Francis a Mexico
Image caption Fafaroman ya bukaci al;umar kasar da su yaki fataucin muggan kwayoyi da kasar ta yi kaurin suna akai.

Fafaroma Francis ya bukaci al'umar Mexico da su inganta kasarsu ta yanda mazauna kasar ba za su yi sha'awar kaura zuwa wata kasa ba, ta yadda matasa ba su fada hannun fataken da da ke halaka jama'a.

Ya yi wannan kiran ne a wajen wani babban taron da aka yi na mutum dubu dari uku a Ecatepec, wurin da ya fi ko'ina talauci da rigingimu a birnin Mexico.

Ya kuma ce zai so gayyace su domin su kasance a sahun gaba wajen tsara dabarun da za su taimaka wajen sauya kasar Mexico zuwa wurin da ake samun walwala, wurin da ba mai sha'awar barinsa.

Harwayau Fafaroman ya ziyarci wani asibitin yara da ke birnin Mexico, kuma daga nan ne ya soma rangadin wasu yankunan kasar masu fama da rikici.