Shin 'yan Boko Haram na samun horo daga Al-Shabab?

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya ce mayakan kungiyar Boko Haram sun samu horo a Somalia.

Shugaba Mahamud ya fadi haka ne a ranar Lahadi a wajen wani taro a Jamus.

Ya kara da cewar 'yan ta'adda na da alaka da juna kuma suna da hadin-kai sosai, don haka kasashen duniya na bukatar hada karfi da karfe domin mayar da martani kwakkwara.

Ya ce a halin yanzu suna da shedar cewar 'yan Boko Haram din sun samu horo a Somalia.

Dr Bawa Abdullahi Wase, wani masani kan harkokin tsaro a Najeriya, ya bayyana yadda yake kallon wannan ikirarin na shugaban Mahamud na Somaliyar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hassan Sheik Mohamud bai bayyana takamaimai lokacin da 'yan Boko Haram suka samu horon a Somalia ba.

A baya dai kungiyar ta Al-Shabab ta bayyana 'yan wasu kasashe ciki har da 'yan Najeriya da ke karbar horo a Somalia.

Sai dai abubuwa sun sauya, a yanzu Boko Haram ta zama wani reshe na kungiyar IS, yayin da Al-Shabab kuma ke ci gaba da kasancewa da Al-Qaida.

Saboda haka abu ne mai yiwuwa a yi tunanin suna tare kamar yadda shugaban kasar Somalia ya nuna.