MDD ta yi allawadai da harin asibitoci a Syria

Image caption Wata kungiya da ke sa ido a rikicin Syria ta ce kasar Rasha ce ta kai harin

MDD ta yi allawadai da hare haren saman da aka kai ranar Litinin kan asibitoci da dama da kuma makarantu a arewacin Syria, wanda ta ce ya hallaka kusan mutane hamsin da suka hada da kananan yara.

An kuma lalata asibitoci uku a hare haren.

Babban Sakataren MDD Ban Ki Moon ya ce wani al'amari ne da ya sabawa dokar kasashen duniya.

Ita ma Washington ta yi allawadai da hare haren wanda ake ta dorawa Rasha alhaki,.

Kungiyar Likitoci ta MSF ta ce an hari daya daga cikin asibitocinta a lardin Idlib, amma wani jami'in diflomasiyyar Syria ya ce Amurka ce ta kai wa asibitin hari ta sama

Kiyasi ya nuna cewa akalla mutum 250,000 suka mutu a shekara biyar da aka kwashe ana yaki a kasar ta Syria.

Kazakila, rahotanni na nuna cewa kimanin mutum miliyan goma sha daya ne suka fice daga kasar tun lokacin da dakarun da ke biyayya ga Shugaba Bashar al-Assad da na 'yan adawa suka kaddamar da hare-hare.