Me ya sa Buhari ya kori shugabannin ma'aikatu?

Gwamnatin Najeriya ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kori wasu shugabannin ma'aikatun gwamnati ne saboda ba sa yin aiki yadda ya kamata.

A ranar Litinin ne dai aka sallami shugabannin ma'aikatu ashirin da shida daga aiki.

Babban mataimaki na musaman kan harkokin yada labarai na shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta dauki matakin ne bayan da ta fahimci cewa shugabannin hukumomin ba za su taka wata muhimmiyar rawa ba a sauyin da take son ta kawo a cikin kasar, kamar yadda za ku ji a hirarsa da Raliya Zubairu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugabannin da aka kora sun hada da: shugabannin gidan talabijin na gwamnatin tarayya, (NTA), da Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN), da muryar Najeriya, da kamfanin dillacin labarai na kasar (NAN), da hukumar sa idanu a kan kafafen watsa labarai na kasar da hukumar wayar da kan jama'a ta kasar (NOA).

Sauran su ne:

 • Hukumar kula da rarar man fetur (PTDF)
 • Hukumar da ke sa ido kan hada kan kasashen Afirka (NEPAD)
 • Asusun samar da Inshora na Najeriya (NSITF)
 • Hukumar tabbatar da ka'ida wajen sayar da kayayyakin Najeriya (NCDMB)
 • Bankin bayar da rance sayen gidaje (FMBN)
 • Asusun tallafawa manyan makarantu (TETFund)
 • Hukumar bunkasa fasarar sadarwa ta Najeriya (NITDA)
 • Asusun daidaita farashin man fetur (PEF)
 • Hukumar kula da jiragen kasa (NRC)
 • Hukumar da ke sa ido a harkokin saye-saye na gwamnati(BPP)
 • Hukumar cefanar da kaddarorin gwamnati (BPE)
 • Hukumar kula da kayyade farashin man fetur (PPPRA)
 • Hukumar da ke sa ido kan ingancin kayayyaki (SON)
 • Hukumar da ke sa ido kan inganci abinci da magunguna(NAFDAC)
 • Hukumar da ke neman masu zuba jari a Najeriya (NIPC)
 • Bankin Masana'antu na Najeriya (BoI)
 • Cibiyar kula da ci gaban mata(NCWD)
 • Asusun bayar da horo kan masana'antuBankin da ke kula da shigowa da fitar da kayayyakiHukumar da ke hana fataucin mutane (NAPTIP)

Goodluck Jonathan ne ya nada akasarin mutanen da aka kora.