BH: Garuruwan da aka kwato na wahala

Image caption Kungiyar ta Boko Haram ta lalata garuruwa da dama.

Mazauna wasu garuruwa da sojojin Najeriya suka kwato daga hannun 'yan Boko Haram sun ce suna fuskantar matsaloli.

Kusan shekara guda ke nan tun bayan da dakarun sojin suka kwace wasu garuruwan da kungiyar Boko Haram ta mamaye a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Sai dai kuma tun bayan kwato su, har yanzu mazauna garuruwan na cewa hanyoyin wasu daga cikin su ba sa biyuwa, sannan mutanen da ke zaune a wuraren na fama da matsaloli da dama.

Garin Gwoza dai na daya daga cikin garuruwan da kungiyar Boko Haram ta kama, wanda daga bisani sojoji suka kwato shi a watan Maris din shekarar 2015.

Duk da an kwato garin, har yanzu ba shiga ba fita sai da rakiyar sojoji.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa har yanzu al'ummar garin na fama da matsaloli da suka hada da rashin abinci da sauran abubuwan more rayuwa.

Mutumin ya ce abin da ke janyo matsalar abincin ita ce idan 'yan kasuwar garin sun fita zuwa wani gari su siyo kaya, to kafin su koma Gwoza a kan dauki lokaci saboda sai sun jira sojoji a wani gari kafin su zo su taho da su zuwa garin nasu, kuma su kan yi akalla makonni biyu zuwa uku kafin sojojin su taho da su.

Sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ma ta jihar Borno da su taimaka a bude musu hanyoyinsu.

Su ma mazauna garin Baga sun ce suna cikin mawuyacin hali na yunwa da talauci da ma rashin abin yi.

A bangaren gwamnati, hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ta ce tana iya bakin kokarinta wajen kawo karshen wannan matsala.

Karin bayani