'An aikata laifukan yaki a Syria'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Assad ya ce tsagaita wuta ba yana nufin kowanne bangare zai daina amfani da makamai ba ne.

Kasar Faransa da Turkiyya sun ce hare-hare ta sama da aka kai a wasu asibitoci da makarantu da ke arewacin Syria, tamkar aikata laifukan yaki ne.

Majalisar dinkin duniya dai ta ce hare-haren - wadanda aka kai da makamai masu linzami -- sun yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 50.

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya dora alhakin kai hare-haren a kan Rasha.

Sai dai Rashar ta musanta kan zargin, kuma kakakin fadar shugaban kasar Dmitry Peskov ya ce "wadanda suka yi zargin ba za su iya bayar da wata hujja da za ta goyi bayan abin da suka ce ba".

'Ina shakka kan shirin tsagaita wuta'

Hakan na faru ne a daidai lokacin da shugaban Syria, Bashar al -Assad, ya nuna shakku a kan ko za a iya aiwatar da shirin tsagaita wutar da aka nemi a yi a wannan makon.

Wasu kasashen duniya masu karfin fada-a-ji ne suka amince a tsagaita wuta a wani taron tsaro da aka gudanar a birnin Munich a makon jiya, amma Shugaba Assad ya ce tsagaita wuta ba ya nufin kowanne bangare zai daina amfani da makami ba ne.

Shugaban ya ce ya kamata duk wani matakin tsagaita wuta ya yi kokarin tabbatar da zaman lafiya, sannan ya dakatar da abin da ya kira 'yan ta'adda daga kara karfinsu a wuraren da suka ja-daga.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria, Steffan de Mistura ya isa birnin Damascus domin kokarin ganin an cimma tsagaita wutar.