An kama babban dan adawa a Uganda

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kizza Besigye ne babban mutumin da ke fafata wa da Yoweri Museveni.

An tsare dan takarar babbar jam'iyyar hamayya a zaben shugaban kasar da za a yi a Uganda na dan wani lokaci, kwanaki kadan kafin a gudanar da zaben.

'Yan sanda sun ce an tsare Kizza Besigye ne saboda ya karya dokar hana toshe hanyoyi.

Sai dai an sake bayan sa'o'i biyu.

Dubban magoya bayansa sun bi jerin-gwanon motocinsa a Kampala, babban birnin kasar a lokacin da yake yakin neman zabe.

Dr. Besigye yana daya daga cikin 'yan takarar zaben da za su fafata da shugaba Yoweri Museveni wanda ya shafe shekara 30 yana mulkin kasar a ranar Alhamis.