An hana yin acaba a Burundi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yin amfani da baburan haya domin kai hare-hare.

Gwamnatin Burundi ta hana yin sana'ar acaba a Bujumbura, babban birnin kasar domin kawo karshen hare-haren da ake yawan kai wa a birnin.

Magajin birnin Bujumbura, Freddy Mbonimpa, ya yi zargin cewa masu aikata laifuka suna yin amfani da baburan acaba domin kai hare-hare.

An kashe wani mutum lokacin da wasu mutane da ke kan babura suka kai hari da gurneti a birnin ranar Litinin.

Kasar ta Burundi ta fada cikin rikici a watan Afrilun da ya gabata lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a karo na uku, sabanin alkawarin da aka yi cewa zai sauka.

Hakan ya sa an rika yin munanan zanga-zanga a kan tituna da kuma yunkurin juyin-mulki, yayin da kusan kullum sai an samu rahotannin kisan mutane a wasu sassa na birnin.