An kashe 'yan Boko Haram 162 a Kamaru

Image caption Kungiyar ta Boko Haram ta dade tana kai hare-hare a Kamaru.

Gwamnatin Jamhuriyar Kamaru ta ce dakarun kasar sun kashe wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne su kimanin 162.

Kakakin gwamnatin kasar, Minista Issa Tchiroma Bakary shi ne ya bayyana haka a Yawunde, babban birnin kasar.

Ya ce an kashe 'yan boko Haram din ne sakamakon wasu hare-hare da sojojin suka kai musu a 'yan kwanakin da suka wuce.

Minista Bakary ya karawa da cewa dakarun nasu sun kuma gano tarin kayayyakin aikin soja da suka hada da makamai.

Kungiyar ta Boko Haram dai ta kara kaimi wajen kai hare-hare a kasar.