"Koriya ta Arewa za ta balbalce"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Park Gun-Hye ta yi gargadin cewa Korea ta arewa zata iya lalacewa idan har taki yin watsi da shirinta na nukiliya

Shugabar Korea ta Kudu Park Gun-he ta yi gargadin cewa Korea ta Arewa zata balbalce idan har taki yin watsi da shirinta na Nukiliya.

Yayinda take jawabi a majalisar dokoki a Seoul, Shugabar ta ce dole ne Pyongyang ta gane cewa burinta na mallakar makamin nukiliya zai yi sanadiyyar rushewar ta ne kawai.

Tace Gwamnati zata dauki kwararan matakai domin Korea ta Arewa ta fahimci cewa kirkirar nukiliya, ba zai taimakawa dorewarta ba, sai dai kawai ya gaggauta rusa gwamnatin kasar

A birnin New York, jakadan korea ta Kudu a majalisar dinkin duniya ya bukaci kwamitin sulhu na MDD ya amince da kakaba mata takunkumi, bayan makamin rokar da korea ta Arewan ta harba a farkon watan da ake ciki.

Ita ma Mai baiwa gwamnatin Amurka shawara kan harkokin Tsaro, Susan Rice, ta ce tana tsammanin China zata goyi bayan daukar tsauraran matakai akan Koriya ta Arewan