"Za mu sauya tsarin mulkin Nijar"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Moden Lumana ta ce za ta yi garambawul ga yadda ayyukan hukumomin Nijar ke tafiya.

A Jamhuriyar Nijar, jam'iyyar Moden Lumana ta ce za ta sauya kundin tsarin mulkin kasar tare da yin garambawul ga yadda ayyukan hukumomin kasar ke tafiya idan ta lashe zaben da ke tafe.

Sakatare Janar na jam'iyyar, Maman Sani Malam Maman, ya shaida wa BBC cewa jam'iyyar za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin bunkasawa da inganta ayyukan noma da kiwo,da kuma amfani da kudin ma'adinai a kan hanyoyin da za su amfani 'yan Nijar idan dan takararta, Hama Amadu, ya zama shugaban kasa.

Shi dai Hama Amadou yana tsare a gidan yari saboda zargin da ake yi masa na safarar jarirai daga kasar Najeriya.

Sai dai Malam Maman ya ce duk da haka ba za su karaya ba a yunkurin da suke yi wajen ganin ya lashe zaben Nijar.