Ali Modu Sheriff ya zama shugaban PDP

Hakkin mallakar hoto Modu Sheriff Twitter

Babban Kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP a ranar Talata ya bayyana sunan Ali Modu-Sheriff daga jihar Borno a matsayin sabon shugaban jam'iyyar

Ali Modu-Sheriff zai maye gurbin Alhaji Adamu Mu'azu

Wannan shawara da kwamitin zartarwar ya dauka ta biyo bayan mika sunan Sanata Sheriff da gwamnonin PDPn suka yi da kuma mambobin majalisar dokoki da kwamitin amintattu da kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Richard Ihediwa mataimaki na musamman ga sakataren yada labaran jam'iyyar, ta ce Sanata Sheriff ya samu mukamin sabon shugaban jam'iyyar na kasa bayan da ya samu kuri'a 60 cikin kuri'u 71 da aka kada

Sanarwar ta kara da cewa lauyan PDP Barrister Emeka Etiaba (SAN) ne ya rantsar da sabon Shugaban jam'iyyar a wani dan kwarkwaryar biki da aka yi a sakatariyar jam'iyyar ta kasa a Abuja.