Obasanjo ya yaba wa Buhari

Hakkin mallakar hoto Nigeria Government
Image caption Obasanjo ya ce Buhari yana da niyyar gayra Najeriya.

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya yaba wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kan matakan da take dauka wajen yaki da matsalar cin hanci da rashawa a kasar.

Cif Obasanjo, ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da wakilin BBC a kasar Uganda.

Tsohon shugaban kasar ta Najeriya ya ce ya bai wa Shugaba Buhari shawara ya tunkari matsalar tabarbarewar tattalin arzikin kasar kamar yadda yake yaki da 'yan ta'adda.

Ya kara da cewa yana zuwa fadar shugaban kasar akai-kai domin bai wa shugaban shawara, kuma yana da yakinin cewa Shugaba Buhari zai kawo sauyi mai amfani ga 'yan Najeriya.

Ga dai yadda hirar ta su ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti