Ana so Ali Modu Sheriff ya zama shugaban PDP

Hakkin mallakar hoto Modu Sheriff Twitter
Image caption Ali Modu Sheriff ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Jiga-jigan babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, suna son a nada tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, a matsayin sabon shugabanta na riko.

Wani babban dan jam'iiyar ta PDP, wanda ya shaida wa BBC hakan, ya ce sai dai kwamitin amintattu na jam'iyyar ba ya goyon bayan nada tsohon gwamnan jihar ta Borno.

Yanzu haka dai kwamitin zartarwa na jam'iyyar ta PDP ya fara wani taro a Abuja, inda a wajen ne za a amince ko kuma a ki amincewa da nada Ali Modu Sheriff din.

PDP dai ta fada rikici ne tun bayan zaben shugaban kasar da aka yi a watan Maris na shekarar 2015, lamarin da ya kai ga saukar shugabanta, Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu.

Bayan saukar tasa ne Uche Secondus ya zama shugaban riko, ko da ya ke wasu manyan 'yan jam'iyyar daga arewa maso gabashin kasar, karkashin jagorancin Ahmed Gulak, tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasar shawara a kan harkokin siyasa, sun kalubalancin nadin nasa a gaban kotu.

Ahmed Gulak dai ya ce kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya bukaci wani daga yankin nasu ya kammala wa'adin Adamu Mu'azu.

Ali Modu Sheriff dai ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ta PDP ne daga jam'iyyar APC, mai mulki.