MDD na so a yi binciken lalata yara a CAR

Image caption MDD na bincike a kan cin zarafin yara a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi Jamhuriyar Demokradiyar Congo da ta gudanar da bincike game da sababbin zarge- zargen da ke cewa sojojin kiyaye zaman lafiyarta sun ci zarafin yara a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Wani mai magana da yawun Majalisar, Farhan Haq, ya ce gwamnatocin kasashe sun bai wa Majalisar aron sojoji ne saboda su yi aikin kiyaye zaman lafiya, don haka yakamata su ladabtar da sojojinsu da suka taka doka.

Mista Haq ya ce ana zargin sojojin Congo da cin zarafin yara hudu tsakanin shekarar 2014 zuwa 2015.

An dai shafe fiye da shekara 10 ana zargin sojojin kiyaye zaman lafiyar na majaliasar da aikata irin wannan danyen-aiki.

Ana kuma zargin Majalisar Dinkin Duniya da rashin daukar mataki domin takawa matsalar birki.