Za a kirkiro sabuwar na'urar wasan Komputa ta Vega+

Image caption Sabuwar na'urar wasan Komputa ta Vega+

Kamfanin da a kwanannan ya bayyana sake kirkiro abin wasan komputa wato ZX Spectrum , ya bayyana shirinsa na kirkirar wata na'urar wadda bata kai waccan girma ba.

Sir Clive Sinclair wanda ya kirkiro da ainihin na'urar, ya na da hannun jari a kamfanin komputa na Retro da ya kirkiro da sabuwar nau'in na'urar ta sa.

Tuni sabuwar na'urar ta samar da kudin da ya kai dala dubu talatin da daya.

Za a sanyawa na'urar ta Vega+ wasanni games har dubu guda, idan har an samu isassun kudin gudanar da binciken kirkirarta.

Kamfanin Retro komputa ya yi bayanin cewa za a iya yin wasannin na'urar a siririyar tlbijin din nan wato LCD, sannan za a iya hadawa da talbijin.

Kamfanin ya cigaba da cewa tuni an riga an gama kirkiro da samfurin na'urar , kuma bada jimawaba za a fito da samfurinta, sannan nan da farkon bazara mai zuwa za a fara kerata.