Masar :Za a rufe cibiyar kula da wadanda aka azabtar

Image caption Za a rufe cibiya ta karshe da ake kula da wadanda aka azabtar a Masar

A Kasar Masar, hukumomi sun bayar da umarnin rufe cibiya ta karshe da ta rage wacce ake kula da mutanen da aka azabtar.

Cibiyar El Nadeem na tattara bayanan mutanen da aka ci zarafinsu da kuma bayarda shawara ga mutanen da aka azabtar tun daga shekarar 1993, amma an bata lokaci zuwa karshen makon gobe da ta rufe.

Hukumomi sun ce cibiyar ta saba dokokin ma'aikatar lafiya.

Shugaban cibiyar Aida Seif Al Dawla ta fadawa BBC cewa an sanya siyasa wajen daukar matakin.

Tace kuma ba za su bi umarnin da aka basu ba.