Rashin aikin yi ga matasan Nijar

A jamhuriyar Nijar, yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki , matsalar rashin aikin yi musamman tsakanin matasa na ci gaba da daukar hankali saboda girman matsalar da kuma illar da take yi wa kasar.

Matsalar rashin aikin yi dai ta sanya 'yan Nijar din da dama kan tafi ci-rani a kasashe daban-daban musamman ma makwabta kamar Najeriya da Libya da Algeria da dai sauransu, inda sukan fada cikin mummunan yanayi, har ma da asarar rayukansu saboda wahala.

Wani rahoto na hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya,UNDP, a baya-bayan nan ya nuna cewa kasar ta Nijar ce ta baya ga dangi a duk fadin duniya, a mizanin jin dadin rayuwa.

A ranar Lahadi mai zuwa ne za a gudanar da zabukan kasar.

Ga rahoton da Ishaq Khalid ya aiko mana daga Damagaram.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti