Donald Trump ba zai zama shugaban Amurka ba —Obama

Hakkin mallakar hoto Reuters Getty
Image caption Obama ya ce shugabancin Amurka ba wasan barkwanci ba ne.

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce mutumin da ke son yin takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump, ba zai zama shugaban kasar ba saboda shugabancin al'amari ne mai girma.

A lokacin da wani dan jarida ya tambayi Shugaba Obama a wajen wani taro a California a kan ko yana gani Mr Trump zai zama shugaban kasar, sai ya ce, "Shugabancin Amurka ba wasan barkwanci ba ne, ba tallata kai ba ne. Zan ci gaba da yin amannar cewa Mr Trump ba zai zama shugaban kasa ba. Abin da ya sa na fadi haka kuwa shi ne, saboda na yi amanna da Amurka".

Mr Trump, hamshakin dan kasuwa, shi ne kan gaba a cikin mutanen da ke son yin takara a karkashin jam'iyyar Republican.

Ya lashe zaben fitar da 'yan takara guda daya, kuma shi ne kan gaba a kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka yi kan wanda zai lashe zaben jihar South Carolina, inda 'yan jam'iyyar za su yi zabe ranar Asabar mai zuwa.

Mr Trump ya mayar wa Obama martani, yana mai cewa ya ji dadi da mutumin da ya kira wanda ya lalata Amurka ya yi tsokaci a kansa.

Mr Trump dai yana so a hana Musulmai shiga kasar ta Amurka.