Obama zai nada sabon alkalin kotun koli

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Obama zai nada sabon alkalin kotun kasarsa

Shugaba Obama ya yi watsi da kiraye-kirayen da mambobin jam'iyyar Republican a majalisar dattawa ke masa na ya bar nadin sabon alkalin kotun kolin kasar.

Mr Obama ya ce zai bayyana sunan wanda zai maye gurbin Justice Antonin Scalia, wanda ya rasu a ranar Asabar, kuma kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadar daga nan kuma ko dai majalisar dattawa ta amince da wanda aka nada, ko kuma ta yi watsi da shi.

Ya ce nan da wani lokaci "ina da niyyar bayyana mutumin da ya dace sosai da wannan mukami, daga nan sai a gabatar da shi gaban kwamitoci, sannan kuma sai a tabbatar da shi."

Shugabannin jam'iyyar Republican -- wadanda ke da rinjaye a majalisar dattawan -- sun ce za su dauki lokaci wajen tabbatar da duk wanda aka zaba har sai sabon shugaban kasar da za a zaba ya fara mulki a cikin shekara mai zuwa.

'Yan jam'iyyar ta Republican sun ce ya kamata a bai wa mutane damar zaben shugaban da Mista Obama zai nada wanda ya dace da wannan mukami.