An soma kai kayan agaji a Syria

Hakkin mallakar hoto

Wani jerin gwanon manyan motocin kai agaji sun soma kai kayyakin da ake bukata ga wasu yankuna biyar da aka yi wa kawanya a Syria.

Wannan wani bangare ne na yarjejeniyar da MDD ke goyawa baya tare da wata kungiyar agaji a Syria domin taimakawa dubban mutanen da rikicin ya rutsa da su.

Akwai rahotannin da ke cewa tuni aka kai agajin zuwa hudu daga cikin kauyuka biyar, biyu daga cikinsu na karkashin ikon 'yan tawaye ne sannan kuma biyu wanda ke karkashin ikon gwamnati.

A wasu yankunan, an ruwaito cewa mutane suna mutuwa saboda yunwa da kuma rashin abinci mai gina jiki.

Gwamnatin Syria ta amince akai agaji zuwa wasu yankuna bakwai da a kai wa kawanya.

Hakan na zuwa mako guda kafin a dawo da tattaunawar zaman lafiyar da ake tsakanin bangarorin syria masu rikici da juna