Bom ya halaka mutane 28 a Turkiyya

Hakkin mallakar hoto .

Wani bom da aka dana cikin mota a Ankara babban birnin Kasar Turkiyya ya hallaka akalla mutane 28 da kuma jikkata mutane fiye da 60.

Jami'ai sun ce bom din ya tashi ne a lokacin da motocin safa- safa na sojoji suka tsaya a inda ake bada hannu dake kusa da majalisar dokoki da kuma shedikwatar sojoji.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda ya soke tafiyarsa zuwa kasar waje ya sha alwashin ci gaba da yaki da wadanda suke kaddamar da hare haren da kuma wadanda suke goya musu baya.

Wata majiyar tsaron Turkiyya ta zargi kungiyar 'yan awaren kurdawa ta PKK da aka haramta.

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce ya kamata kawayen NATO su tsaya kafada da kafada a yakin da ake yi da ta'addanci.