Shugaba Buhari zai kai ziyara Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Buhari zai je Masar halartar taro

Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria zai bar Abuja a ranar Juma'a zuwa wurin shakatawar nan na Sharm El-Sheihk a kasar Masar, domin halartar taron kasuwanci na Afrika.

A ranar Asabar ne dai za a bude taron wanda gwamnatin Masar ta shirya karkashin hukumar Tarayyar Afrika.

Daga cikin wadanda za su yi jawabai a taron sun hada da Shugaba Buhari da Shugaban Masar Abdel Fatah al-sisi.

Sauran su ne shugabannin kasashen Togo da Sudan da Kenya da Gabon da Equitorial Guinea da kuma Firai ministan kasar Habasha.