CBN ya yi karin haske kan kudaden waje

Hakkin mallakar hoto Getty

Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ce ba abin da ya hada shi da sayar wa daidaikun mutane ko kamfanoni kudin musaya na kasashen waje.

Babban bankin yana mai da martani ga zargin da shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji AbdulSamad Isyaku Rabi'u ya yi cewa, babban bankin ba ya bai wa wasu 'yan kasuwa abin da suke bukata na dala domin su samu damar sayo kayayyakin da za su sarrafa.

Ga karin bayanin da kakakin babban bankin Alhaji Ibrahim Mu'azu ya yi wa BBC dangane da wannan batu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti