Mutane 71 sun mutu a hatsarin mota a Ghana

Image caption Hatsarin ya faru a Kintampo da ke da nisan kilomita 420 daga birnin Accra

Kimanin mutane 71 ne suka rasa rayukansu bayan wata mota kirar bus ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota a Ghana, in ji hukumomin kasar.

Haka kuma mutane 23 sun jikkata a hatsarin na ranar Laraba da daddare, wanda kuma aka kwashe shekaru ba a ga irinsa ba a kasar.

Shugaba John Dramani Mahama, ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka mutu a shafinsa na Twitter.

'Abin da ya janyo hatsarin'

Kwamishinan 'yan sandan yankin Brong Ahafo, Maxwel Tindani ya shaida wa gidan rediyon joy FM cewa, motar bus din ta samu matsalar birki, amma direban ya debi fasinjoji ba tare da an gyara ba.

Kuma motar na kan hanyarta ne ta zuwa birnin Tamale lokacin da ta kara wa babbar motar da ke makare da kwandunan tumaturi.

Tuni dai jami'an 'yan sanda da sojoji suka isa inda lamarin ya faru, domin aikin ceto.

Kuma hukumomin kasar sun fara bincike kan makasudin hatsarin.