'Yan kasuwar 'Singer' a Kano sun tafka asara

Gobara ta lalata dukiya ta miliyoyin naira a kasuwar 'Singer' da ke jihar Kano a arewacin Nigeria.

Gobarar wacce ta soma ci tun cikin dare a ranar Laraba, ta janyo hasarar dukiya mai dumbin yawa.

Bayanai sun ce kawo yanzu ba a gano abin da ya janyo gobarar ba.

Sai dai wani mai shago a kasuwar, Alhaji Auwal Gabari Jakada ya shaida wa BBC cewar "Gobarar ta tashi ne tun da kusan misalin karfe hudu na daren ranar Laraba."

Alhaji Auwal ya kara da cewar "Muna ganin an yi hasarar dukiyar da ta kai ta Naira biliyan biyar."

Bayanai sun ce jami'an kashe gobara na ci gaba da kokarin kashe gobarar.

Ga rahoton da Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana daga Kano

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti