'Kurdawa ne suka kai harin Ankara'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ahmet Davutoglu ya ce mayakan Kurdawan sun samu taimako ne daga takwarorinsu na kasar.

Firai Ministan Turkiyya, ya yi zargin cewa mayakan kungiyar Kurdawa ta YPG da ke da reshen a Syria ne suka kai mummunan harin bama-bamai a birnin Ankara ranar Laraba.

Ahmet Davutoglu, wanda ya bayyana cewa an kama mutum tara da ke da alaka da kai harin, ya kara da cewa mayakan sun hada kai ne da takwarorinsu na Kurdistan Workers Party (PKK) da ke kasarsa.

Dakarun kasar ta Turkiyya sun kai hare-hare a kan 'yan kungiyar ta PKK a arewacin kasar Iraki ranar Laraba.

A gefe guda kuma, wani bam da aka jefa ya sauka kan wata tawagar motocin sojoji a kudu maso yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji shida.