Yunkurin shawo kan tsananin damuwa a Zimbabwe

Hakkin mallakar hoto Thembela Nymless Ngayi
Image caption Wakilin BBC ya tattauna da Malama Chipo kan abin da ya jefa ta cikin matsananciyar damuwa.

A kasar Zimbabwe ana gudanar da wani shiri domin taimakawa dubban mutanen da ke fama da tsananin damuwa.

Shirin na musamman wanda ake kira 'The Friendship Bench' , ya kunshi ma'aikatan kiwon lafiya, da masu aikin sa-kai, da likitocin masu tabin-hankali.

Wakilin BBC, Brian Hungwe, ya bi diddigin wannan kungiya domin ganin yadda take tafiyar da ayyukanta.

Da farko ya gana da wacce ta warke daga cutar ta tsananin damuwa, Malama Chipo, mai 'ya'ya biyar, wacce ta bayyana halin tsananin damuwar da ta shiga bayan mutuwar aurenta.

Ta ce, ''Lamarin ya faru ne bayan maigida na ya fara mu'amala da wasu 'yan mata a waje, saboda haka a duk lokacin da ya dawo gida sai mu yi da fada da shi.Ya kan fita bai bar mana abinci ba, kuma tun daga wannan lokaci na fara shiga tsananin damuwa, har ta kai ga kwantar da ni a asibiti.Na kamu da rashin lafiyar da har na kusa mutuwa".

Shekaru 10 kenan da fara shirin na '' Friendship bench'', kuma ya taimaka wa sama da mutane dubu 10 a Zimbabwe.

Masu shirin suna aiki tare da kananan asibitocin kula da lafiya, da kan tura marasa lafiyar zuwa cibiyar Friendship Bench, wacce ke wajen asibitocin, inda ma'aikatan kiwon lafiya da aka fi sani da Golden Ladies Grandmothers da aka horas kan ayyuukan shawo kan matsalolin ke tafiyarwa.