Sojoji sun gano kasuwar 'yan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption 'Yan Boko Haram ne ke saye da sayarwa a kasuwar

Kimanin mutane 195 da dabbobi kusan 500 ne aka ceto daga sansanonin 'yan Boko Haram da ke jihar Borno, a cewar rundunar sojin Najeriya.

Hakan dai ya biyo bayan ci gaba da lalata sansanonin 'yan kungiyar da sojojin kasar suka ce suna yi.

Wata sanarwar rundunar dauke da sa hannun kakakinta, Kanar Sani Usman Kuka Sheka ta ce, sojojin sun lalata sansanoni takwas a kananan hukumomin Dikwa da Bama a jihar Borno, a ranar Laraba.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Akwai dabbobi da dama a kasuwar

Sanarwar ta kara da cewa a Gulumbu, daya daga cikin sansanonin sun gano dakin shan magani da wata babbar kasuwa a Gulumba da kuma babban janareta Mikano da kekuna 750 da babura 180 da manyan motocin daukar kaya biyu.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Asibitin 'yan Boko Haram
Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Sojoji sun ce sun yi nasarar kubutar da mutane 195

A cewar sojin, sun kashe 'yan Boko Haram da dama kuma sun gano kakin sojoji da makamai da albarusai a sansanonin mayakan kungiyar.