'Yan PDP a Borno sun soki zaben Sheriff

Image caption Shugabancin jam'iyyar PDP

A Najeriya, wasu 'ya'yan jam'iyyar PDP sun ce babu yawunsu a zaben Sanata Ali Madu sharif a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na kasa.

Reshen jam'iyyar na jihar Borno, wato asalin jihar sabon shugaban ya bai wa jam'iyyar ta kasa wa'adin nan da ranar Laraba su kira taro ko kuma 'yan PDP na jihar su zauna su dauki nasu mataki.

Tuni dai kwamitin amintattun jam'iyyar PDP shi ma ya nisanta kansa da zaben Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban jam'iyyar.

Alhaji Baba Basharu, shi ne shugaban jam'iyyar PDP na jihar Borno ya ce ba su da masaniya game da nadin da za a yiwa Ali Madu Sheriff, sai ji kawai suka yi an nada shi sabon shugaban jam'iyyar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti