An fara kada kuri'a a zaben shugaban Uganda

Image caption Shugaba Museveni yana fuskantar kalubale daga wajen 'yan takara bakwai.

An bude rumfunan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Uganda.

Ana tsammanin Shugaba Yoweri Museveni ne zai sake lashe zaben, inda zai tsawaita wa'adin mulkinsa.

Sai dai yana fuskantar kalubale daga 'yan takara bakwai.

Kuri'ar jin ra'ayoyin jama'ar da aka gudanar na nuna cewa zai lashe kashi hamsin cikin dari domin kaucewa zuwa zagaye na biyu.

Dan takarar babbar jam'iyyar adawa, Kizza Besigye, ya ce ba ya sa ran za a gudanar da zabe na gaskiya da kuma adalci.