Ghana: Za a yi bincike kan hadarin mota

Hakkin mallakar hoto Albert Azongo
Image caption Hadarin motar ya faru ne a kan babbar hanyar Kintapo zuwa Tamale a farkon watan nan a in da aka yi hasarar rayuka, wasu kuma suka jikkata.

Shugaban Ghana John Dramani Mahama, ya bukaci hukumar 'yan sandan kasar da ta hada gwiwa da hukumar kiyaye haddura domin su gudanar da bincike dangane da afkuwar wani mummunan hadarin mota da ya faru a kasar.

Shugaban ya bukaci hakan ne a yayin da ya ke rantsar da sabon shugaban 'yan sandan Ghana Mista John Kudalor.

A cewar Shugaba Mahama, za a gudanar da binciken ne domin a fito da gaskiya sanadiyar afkuwar hadarin, da kuma kawar da rade-radi, da kuma zarge-zarge.

Kimanin mutane 71 ne suka rasa rayukansu bayan wata mota kirar bus ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota a Ghana, in ji hukumomin kasar.

Mummunan hadarin ya faru ne akan babban hanyar Kintapo zuwa Tamale a in da aka yi hasarar rayuka.