Zan iya bude makullin sirrin iPhone-McAfee

Image caption Mcafee shi ne ya kirkiri kariya ga cutar komfuta

Mutumin da ya kirkiri kariya ga cutar komfuta, wato virus, John McAfee ya ce za iya wargaza makullin da ke tsare sirri a cikin wayar iPhone, mallakin Syed Farook, dan bindigar da ya kai harin San Bernardino, a Amurka.

John McAfee ya yi wannan tayin ne ga hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, wato FBI a cikin wata kasidar da aka wallafa a jaridar Business Insider.

Kamfanin Apple dai ya ki bin umurnin da wata kotu ta ba shi cewa ya cire makangar sirrin wayar Syed Farook, lamarin da ya raba kan jama'a ta fuskar ra'ayi dangane da ko ya dace a tilasta wa kamfanin ya bude sirrin ko kuma a'a.

Shi da John McAfee ya ce shi da ayarinsa za su yi dawainiyar bude wayar ba tare da karbar ko da sisin kwabo ba.

Kuma ya yi wannan tayin ne a daidai lokacin da yake yakin neman tsayawa takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Libertarian Party, yana cewa aikin bude wayar zai dauke mako uku.

Sai dai wasu kwararru na nuna shakku dangane da ikirarin John McAfee, suna cewa wayar iPhone na da wuyar kutse idan aka kwatanta ta da sauran wayoyi.