'Yan Mozambique na neman mafaka a Malawi

Hakkin mallakar hoto EPA

Fiye da 'yan kasar Mozambique dubu shida ne ke neman mafaka a sansanonin 'yan gudun hijrar da ke makwabciyarta Malawi.

Sun ce suna tserewa tashin hankalin da ke faruwa ne a 'yan kwanankin nan a arewacin kasar tsakanin gwamnati da kuma mayakan 'yan adawa wadanda suka fusata bayan rikicin daya biyo bayan zaben kasar a shekarar 2104.

Akwai rahotannin da ke cewa mahukuntan Mozambique sun ce 'yan gudun hijrar wadanda fari ke tursasa musu barin gidajensu, sune ke shiga sansanonin 'yan gudun hijrar a Malawi kuma ake tursasa musu koma gida.

Hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar dinkin duniya ta ce 'yan Mozambique da jami'an kasar sun sabawa dokokin kasa da kasa ta hanyar zuwa sansanin 'yan gudun hijirar Malawi ba tare da sun sanar ba, kuma hukumar ta bukace su da su koma gida.