An tsare shugaban 'yan adawar Uganda

Image caption Shugaba Museveni na kan gaba a kuri'un da aka kirga

'Yan sanda a Uganda sun tsare babban dan adawa a zaben shugaban kasar Uganda, kwana guda bayan kammala zabe, in ji wakiliyar BBC da ke inda lamarin ya faru.

An kama Kizza Besigya ne a lokacin wani samame da aka kai a shalkwatar jam'iyyar da ke Kampala babban birnin kasar, a lokacin yana gab da soma jawabi a taron manema labarai.

Rahotanni sun ce an harba barkonon tsohuwa a wajen ginin jam'iyyar.

Shugaba Yoweri Museveni ne ke kan gaba a yawan kuri'u, bayan da aka kirga daya bisa hudu na kuri'un da aka kada.

Mista Museveni na neman wa'adin mulki a karo na biyar ne, bayan ya shafe shekaru 30 a kan mulki.