Trump ya yi nasara a South Carolina

Mr Trump
Image caption Kalaman da Mr Trump ya yi kan hana Musulmai shiga Amurka baki daya, ya janyo cece-kuce.

Mai neman tsayawa takarar shugabancin Amurka a karkashin Jam'iyyar Republican, Donald Trump ya samu nasara a zaben fidda-gwanin da ake yi a jihar South Carolina.

Mista Trump dai ya lashe kashi daya bisa ukun kuri'un da aka kidaya.

Mutum biyu da ke rufa masa baya, wato Ted Cruz da Marco Rubio suna tafiya kafada-da-kafada da juna, yayin da farauta ta ki tsohon Gwamnan jihar Florida, Jeb Bush, kasancewarsa na hudu, har ma ya sanar da cewa zai fice daga yakin neman zaben.