An bude rumfunan zabe a Niger

Ana tantance masu kada kuri'a
Image caption Zaben na jamhuriyar Nijar ya dauki hankalin kasashe makofta, irin su Najeriya.

A jamhuriyar Nijar, an bude rumfunan zabe, inda ake tantance masu masu jefa kuri'a fiye da muliyan bakwai wadanda za su kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki.

Shugaba na yanzu Muhamadou Issoufou na neman wa'adi na biyu na shekaru biyar.

Yan takara goma sha hudu ne ke kalubantarsa, kuma cikin 'yan takarar na jam'iyyun adawa, har da tsofofin Firayim ministoci uku.

Idan dai ba a samu dan takara da ya samu fiye da kashi hamsin cikin dari na illahirin kuri'u da aka kada ba, to wajibi ne a gudanar da zabe zagaye na biyu tsakanin 'yantakara biyu da suka fi samun kuri'u.

Hukumomi dai sun bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da zaben.

Wannan na zuwa ne yayin da kotun koli ta yi watsi da wata kara da 'yan adawa suka shigar suna neman a tilasta amfani da katin shaidar 'dan kasa, ko fasfo ko kuma takardar shaidar tuki wajen jefa kuri'ar, idan ana tababa kan sahihancin katin zaben mutum, a maimakon tsarin da aka yi amfani da shi a zabukan baya, na gabatar da mutane biyu shaidu, su tabbatar da sahihancin mai jefa kuri'a.

Za a gudanar da zaben ne yayin da daya daga cikin 'yan takara na adawa watau Hama Amadou ke tsare a gidan yari bisa zarginsa da safarar jarirai daga Nijeriya, amma ya musanta zargin.