Museveni ya lashe zaben Uganda

Shugaban Uganda Yoweri Museveni Hakkin mallakar hoto Yoweri Museveni Facebook
Image caption Shugaban Uganda Yoweri Museveni

Hukumar zabe ta kasar Uganda ta baiyana shugaba Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Zai sake yin wa'adin shekaru biyar a karagar mulki, karo na biyar a matsayin shugaban kasa.

Masu sa ido na kasa da kasa sun soki lamirin yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar da na yan majalisar dokoki.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obanasanjo wanda ya kajoranci tawagar kungiyar kasashe renon Ingila Commonwealth ya ce zaben ya gaza wajen bada dama ta bai daya ga yan takara, da nuna siyasar kudi da amfani da kayan hukuma ta hanyar da bata dace ba da kuma ayar tambaya kan cancantar hukumar zaben na gudanar da adalci.

A nasa bangaren wakilin kungiyar tarayyar turai da ya sa ido kan zaben Jo Leinen yace an gudanar da zaben cikin yanayin tsoro da firgici da kuma rashin adalci wajen bada yancin fadin albarkacin baki a kafofin yada labarai.