'Zaben Uganda bai gansar ba'- Obasanjo

Shugaba Yoweri Museveni Hakkin mallakar hoto
Image caption Common Wealth ba ta gansu da sahihancin zaben ba.

Tawagar kungiyar Common Wealth da ta sa-ido a kan zaben shugaban kasar da aka gudanar, sun ce ba su gamsu da yadda aka tafiyar da zabe a kasar ba.

Tawagar, wadda tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya jagoranta, ta ce tana tababa game da kwarewar hukumar zaben Uganda wajen gudanar da sahihin zabe.

Cif Obasanjo ya ce duk da an samu mutane da dama da suka tsaya takarar neman shugabancin kasa ba su samu sarari ba dan yawo a cikin gari, kuma 'yan adawa ba su samu walwala ba a lokacin zaben.

Ya bayyana hakan da rashin samun isassun kudade daga bangaren 'yan adawar, dalilin da ya sa ba su yi wani abun a zo a gani ba a lokacin zaben.

Masu sa ido na kungiyar Common Wealth sun nuna damuwa kan yadda jam'iyya mai mulki ke ci gaba da yi wa abokan hamayyar ta fintinkau, wanda hakan ke yin illa ga 'yancin jam'iyyun siyasa wajen fadar albarkacin bakin su.