Shugaba Buhari na ziyara a Saudiyya

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Buhari ya kai ziyarar ne dan kulla huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

A yau ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tashi zuwa Saudi Arabia, inda zai fara wata ziyara ta kwana biyar.

Yayin ziyarar dai ana sa ran Shugaba Buharin zai gana da Sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud da manyan jami'an gwamnatin Saudiya, kuma kan gaba a cikin batutuwan da za su tattauna shi ne batun farashin man fetur a kasuwannin duniya.

A yanzu dai Najeriya, wadda ta dogara da man fetur don samun galibin kudin-shigarta, na fama da matsin tattalin arziki sakamakon mummunar faduwar farashin man ya yi.

Mai taimaka wa shugaban Najeriya a kan al'amuran yada labarai, Garba Shehu, ya shaidawa BBC ce wa Sarki Salman Bin Abdul'azeez ne ya gayyaci shugaba Buhari domin tattaunawa akan batutuwan da suka shafi Najeriya.

Muhimmi a ciki shi ne batun farashin man fetur, da bunkasa huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, da zuba jari a bangaren harkar Noma da wutar lantarki duk dai a Najeriyar.