Fargabar matsalar ruwa a birnin Delhi

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumomin India sun tura sojoji kimanin dubu goma zuwa jihar Haryana domin shawo kan wata tarzoma da ta yi sanadiyar mutuwar mutane goma da kuma ke barazana ga kafofin samar da ruwa zuwa Delhi babban birnin kasar.

Al'ummar Jat wadanda ke korafi kan basu kason guraben ayyuka sun rufe manyan hanyoyi da gidajen mai tare kuma da kone konen motoci.

Wata mace a Rohtak daya daga cikin garuruwa tara da aka sanya dokar takaita zirga zirga ta baiyana halin da ake ciki a matsayin mummunan ta'asa

Ta ce abincinta ya kusa karewa kuma babu wanda ke tsawartar wa masu zanga zangar domin hana su kwasar ganima.