Niger: Ana ci gaba da zabe a Tillaberi

Image caption Mata a layin zabe suna jiran kada kuri'unsu.

Ana ci gaba da kada kuri'a a yankunan Tillaberi da Tahoua na Jamhuriyar Nijar.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijar, CENI ce ta bayar da umurnin gudanar da zaben saboda ba a kai kayan aiki a kan kari a yankunan ba.

A ranar Lahadi ne dai aka gudanar da zaben shugaban kasar da na 'yan majalisar dokoki a dukkanin sauran yankunan kasar.

Yanzu haka kuma ana ci gaba da tattara sakamakon zaben.

Hukumomin kasar sun ce an jinkirta kidayar kuri'un, dan bai wa sauran ma'aikatan hukumar zaben kasar CENI da ke sassa daban-daban na kasar damar kawo sakamaon da suka tattara.

An gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, babu yamutsi ko tada zaune tsaye.

Fatan 'yan kasar dai shi ne hukumar zabe ta yi adalci wajen fadar sakamakon, su kuma 'yan takara kowa ya rungumi sakamakon da ya samu da hannu biyu ba tare da an yi hatsaniya ba.