Kerry: Za a cimma tsagaita wuta a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace ya yi imani an cimma yarjejeniya ta wucin gadi a kan sharduddan tsagaita wuta game da rikicin Syria.

Ya yi wannan kalamin ne a Jordan jim kadan bayan ya yi magana da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov.

Mr Kerry yace yana sa ran shugaba Obama da shugaba Putin za su tattauna cikin kwanaki masu zuwa domin kammala abin da ya kira yarjejeniya bisa manufa.

Tun da farko manyan shugabannin kasashen duniya da na Gabas Ta Tsakiya sun amince yayin wani taro a cikin wwannan watan a birnin Munich domin kawo karshen fadan.

Sai dai wa'adin da aka sanya na ranar juma'a ya wuce ba tare da yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki ba.