Terry ya ji rauni a cinyarsa

Hakkin mallakar hoto Getty

Kyaftin din kungiyar kwallo kafa ta Chelsea John Kerry ba zai samu damar taka leda a karawar da zasu yi da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ba sakamakon raunin da ya ji a cinyarsa.

Terry ya ji rauni a karawar da suka yi da kungiyar kwallon kafa ta New caslte a makon daya gabata.

Cocin Manchester City Manuel Pellegrini ya ce manyan 'yan wasansa ba za su taka leda ba amma zai yi amfani da matasa irinsu Bersant Celina da kuma Manu Garcia a karawar da za su yi ranar Lahadi

Dan wasan Chelsea Bacary Sagna ya dawo kulob din Chelsea bayan raunin da ya samu a gwiwarsa kuma ya soma atiseye da sauran 'yan wasa.